GIABA ta shirya taron duba rayuwar mata a Ghana
December 17, 2024Kungiyar yaki da safarar haramtattun kudade da ayyukan ta’addanci ta GIABA tare da taimakon kungiyar kula da ci gaban mata a karkashin kungiyar ECOWAS, sun shirya wani taron kara wa juna sani da ya mai da hankali ga mata a Accra babban birnin kasar Ghana.
Kamar yadda masu azancin magana kan ce mata in babu su babu gida, saboda baiwar da Allah Ya ba su. A sakamakon hakan ne a bayyanin Dr. Jeffery Isima shugaban kula da ayyukan gudanarwa na kungiyar GIABA, ya ce lokaci ya kai da ya kamata a dama da iyaye mata saboda muhimmancinsu.
Taron ya samu halartan mata kusan 30 daga kasashe 15 wadanda ke shugabanci mai’aikatun gwamnati da hukumar tsaro da ’yan kasuwa da kuma hukumomi masu zaman kansu.
A lokacin da shugaba mai magana da yawun ministan hukumar kula da mata da yara kanana ta Ghana, Madam Dakuwa Newman ta daukaka kira ga gwamnatotin kasashen Afirka da su kara mata a cikin duk tsare–tsaren tattalin arziki.
A hannu dayan kuma Madam Salamatu Thiam , shugaba mai kula da cigaban mata a kungiyar ECOWAS ta jaddada muhimancin wannan taro. Karshen taron na kwanaki uku ana sa ran kwalliya ta biya kudin sabulu, wajen kirkiro da mafita ta rage wannan matsala.