1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gibi a tattaunawar shirin nukiliyar Iran

September 8, 2014

Kungiyar kasashen Turai ta EU ta ce har yanzu akwai babban gibi tsakanin Iran da kasashen duniya dangane da tattaunawar da ake yi kan shirinta na nukiliya da ke cike da takaddama.

https://p.dw.com/p/1D8zm
Iran Atom Archiv 20.01.2014 Natanz
Kasashen da dama na zargin Iran da kokarin kera makaman nukiliya amma ta musanta hakaHoto: Kazem Ghane/AFP/Getty Images

Kantomar kula da harkokin waje ta kungiyar ta EU Catherine Ashton ce ta ambata hakan ranar litini ga manema labarai bayan da ta kammala wata zantawa da ministan harkokin wajen kasar Kanada John Baird, inda ta ke cewar ta na da yakinin cewa nan gaba za a iya kaiwa ga samun fahimtar juna da ma kawar da dukannin banbance-banbancen da ke akwai tsakanin bangarorin biyu.

Sun dai shafe tsawon lokaci ana duba yiwuwar samun daidaito kan shirin na nukiliyar Iran din wanda kasashen duniya musamman ma Amirka da Isra'ila ke dari-dari da shi ko da dai Iran din ta ce shirin nata na zaman lafiya ne, hasali ma ta na yinsa ne da zummar samar da makamashi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu Waba