Gidan sarauta: Taron kungiyar G7 a Schloss Elmau
Tun daga ranar 26 ga watan Yuni ne ake gudanar da taron koli na G7 a karo na biyu a gidan sarautar Alpine nnaSchloss Elmau da ke kudancin Jamus. Me ya sa wannan otal mai alfarma ya zama na musamman?
Yanki mai kyau!
Wannan wuri ne mai daraja da ya ke da muhimmanci a yi bayani a kai. Schloss Elmau ko shakka babu ya cika sharudda guda uku: Gidan sarautar na cikin Jamus a kusa da kan iyakar Austriya, kimanin kilomita 100 kudancin Munich a daya daga cikin tsaunuka masu ban sha'awa. Wuri ne na alfarma ga masu son zama cikin natsuwa da shugabannin kasashe.
Hasken rana? Ba shi da mahimmanci!
Ko da rana ba ta fito ba, wajen na da haske sosai. A ko ina baki za su iya samun kujerun kwanciya na alfarma a karkashin laima, don shakatawa cikin nutsuwa da hangen tsaunukan. An yi wa gidan sarautan lakabi da sunan "The Hideaway," watau "Maboya" saboda ingancinsa da alfarmarsa.
Babu fargabar cunkoso
Sunan wurin ya dace sosai, saboda wajen kashi 35% na otel din ne ake iya bada haya, wanda ba kasafai ba ne ga irin wannan babban otel. Mafi yawan yankin na jama'a ne, shi ya sa ba a taba samun cunkoso a Schloss Elmau. Wannan falo (a hoton) na daya daga cikin wuraren da jama'a ke taruwa, sannan akwai dakin karatu da kantin sayar da littattafai da tufafi da sauransu.
Wasa don zama
Har ila yau Schloss Elmau na da dakin kade-kade da wake-wake da ake yi fiye da 200 a duk shekara, wanda ke kasancewa daya daga cikin manyan masu shirya kade-kade a Jamus. Wani al'amari na musamman shi ne cewa mawakan da suka yi wasa a nan ba sa karbar kudi, amma suna iya zama a cikin otel din kyauta. Kuma baki na iya kallo kyauta.
Benci na katako mai tarihi
Wannan hoton ya yadu sosai lokacin taron G7 na karshe da aka yi a Schloss Elmau a shekarar 2015. Ya nuna shugaban Amurka na lokacin Barack Obama yana zaune a kan benci yayin da tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke bayyana masa hanyoyin rayuwa ko kuma girman bencin. A yanzu haka bencin da ke gaban otel din ya zama fitaccen wurin yin hoto.
Wadannan kananan tebura fa?
Da jimlar dakunan cin abinci tara, Schloss Elmau yana da wani abu muhimmi na la'akari da kowane dandano, a karkashin jagorancin kwararrun masu dafa abinci. Bayan nauo'in abinci kala-kala har zuwa 12, ana bada muhimmanci ga sauran kayan makulashe. Kowane tebur yana da karamin tebur a gefe na ajiye jakunkuna kawai.
Zababbun wuraren hutu
Duk da cewar wannan dakin da aka kebe na Hamam ya yi kama da wurin gyaran jiki, ya sha banban da cikin gidan wankan gyaran fata. Katafaren dakin na mita 500 na da dakunan gyaran jiki guda hudu, da dakunan wanka biyu, da falon shan shayin Larabawa da wurin yin tausa ga wanda ke muradi. Bayan taron na G7 tabbas akwai wasu shugabannin da za su bukaci hutawa.
Otel a cikin otel don muradun taron G7
A 2015, Schloss Elmau ya kaddamar da wani bangaren oten din a matsayin na G7 mai suna "The Retreat." Yana da nisan mita 100 daga ainihin otel din "The Hideaway," mai dauke da kananan gidaje 47, wanda ke bai wa shugabannin duniya damar su kasance da junansu. A taron G7, kowane shugaban kasa zai samu dakunan sauka tare da mataimakansa. Kana saura su zauna a "The Hideaway."
Da irin wannan wuri, babu bukatar TV
Idan kana kallon tsaunin Wetterstein da kewayensa daga tagar dakin kwanciyarka ta ko wace kusurwar wannan otel baka bukatar talabijin duk da cewar akwai daya a kowane daki. Kowane sashi na masaukin mahalarta taron na da falo da kwararo da dakunan ajiye kaya da wasu kananan. Duk da cewar otel din na da abubuwa na musamman, yankin da yake da kewayensa shi ma wani abun sha'awa ne.