Gidauniyar Bill Gates ta ba da tallfin domin yaƙi da Ebola
September 11, 2014Talla
Waɗannan kuɗaɗe dai za a ba da su ga ƙungiyoyin Majalisar Ɗinkin Duniya domin sayen magunguna da kayayyakin aiki waɗanda suka yi ƙaranci domin yaƙi da cutar ta Ebola.
Yazuwa yanzu cutar ta Ebola ta kashe mutane sama da dubu 2300 a cikin ƙasashen Gini da Saliyio da Laberiya da kuma Najeriya. Ko da shi ke ma hukmar ta ce ana buƙatar sama da biliyan 500 domin yin aikin shawo kan cutar a nahiyar Afirka amma dai da alama waɗannan kuɗaɗe za su taimaka sossai.