1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar kasa ta halaka mutane a Taiwan

Yusuf BalaFebruary 6, 2016

Wasu rahotanni na cewa an samu mutane bakwai da suka rasu a wannan girgizar kasa da ta afku a Taiwan. Abin da ake ganin zai iya karuwa nan gaba.

https://p.dw.com/p/1Hqmd
Taiwan starkes Erdbeben
Ma'aikatan agaji na aikin jinkaiHoto: picture-alliance/dpa/W. Santana

Sama da mutane biyar sun halaka a wata girgizar kasa mai karfi maki 6.4 a ma'aunin Richter da ta afka wa yankin kudancin Taiwan da sanyin safiyar Asabar nan, kamar yadda mahukunta suka bayyana.

Wani gini mai hawa 17 da mutane kimanin 200 ke cikinsa ya rushe a birnin Tainan na lardin Yungkang, gine-gine da dama ne dai suka rushe a wannan birni bayan wannan girgiza da ta faru kusan karfe hudu na safiya.

Lai Ching-te waqnda shi ne magajin garin birnin na Tainan ya ce "A aikin agajin gaggawa da ake yi, mutanen da ke cikin baraguzai na gininsu ne za a ba wa fifiko" .

Sashin agajin gaggawa a yankin ya bayyana cewa mutane hudu ne suka rasu da wata jaririya mai watanni goma a duniya. A cewar sashin agajin gaggawar akwai mutane 350 da suka samu raunika wadanda tuni aka garzaya da su asibiti a Kudancin na Taiwan, adadin da ake sa ran zai iya karuwa.