Girgizar kasa ta hallaka mutane da dama
October 26, 2015Talla
Rahotanni daga kasar Pakistan sun nuan cewa kusan mutane 20 suka hallaka sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 7.5, wadda ta faru tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan. Akwai yara 'yan makaranta mata 12 da suka gamu da ajalinsu sanadiyyar tirmutsitsi da ya biyo bayan girgizar kasa a Afghanistan lokacin da suke yunkurin tserewa daga wajen da lamarin ya faru, sannan wasu dalibai kusan 40 suka jikata.
Gwamnatin Firaminista Nawaz Sharif ta Pakistan ta aiwatar da dokar ta baci tare da tura sojojin domin kai dauki inda aka samun faruwar lamarin na wannan Litinin. A gaba daya ana tunanin an samu asarar rayuka fiye da 50 yayin da wasu mutane masu yawa suka samu raunika, tare da salwantar dukiya mai yawa.