1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar kasa ta yi kisa a Turkiyya

February 6, 2023

Fiye da mutane 100 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata girgizar kasar da ta afku a garin Gaziantep da ke kan iyakar Turkiyya da Siriya.

https://p.dw.com/p/4N8Li
Türkei | Erbeben 2011 | Van
Hoto: Evrim Aydin/AP Photo/picture alliance

Rahotanni daga kudancin Turkiyya sun tabbatar da mutane fiye da 100 sakamakon wata girgizar kasa mai karfin maki 7.8 da ta afku a birnin Gaziantep da ke kan iyaka da kasar Siriya. Alkalumma sun kuma nuna wasu fiye da mutum 200 sun jikkata. Ministan kiwon lafiya na Siriya, Ahmad Dumeira ya ce a kalla mutane 41 suka mutu a wani yanki da ke karkashin ikon gwamnati, yayin da likitoci suka tabbatar da mutuwar wasu gommai a yankin da ke hannun 'yan tawaye.

An tura da masu aikin ceto daga Siriya da kuma Turkiyya domin ci gaba da neman wadanda suka makale cikin baraguzan gine-gine. Kimanin gine-gine 130 ne suka lalace sakamakon girgizar kasar a Turkiyya yayin da kafofin yada labarai a Siriya suka ruwaito rushewar tarin gine-gine a Aleppo da kuma Hama. Cibiyar kiyaye aukuwar girgizar kasa ta Siriya ta bayyana girgizar kasar a matsayin mafi muni a tarihin cibiyar. Hukumomi sun kuma ce za a iya jin motsin kasa har a kasashen Lebanon da Cyprus da kuma Masar.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya mika sakon jajensa ga wadanda iftila'in ya rutsa da su. Kawo yanzu dai Turkiyya ta sanya dokar ta baci a kasar.