1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar kasa ta yi kisa a Turkiyya

February 23, 2020

Wata girgizar kasa da ta auku a gabashin kasar Turkiyya, ta kashe mutane a wani birni da ake kira Van mai iyaka da Iran, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

https://p.dw.com/p/3YEuA
Turkei Van | Erdbeben an der Grenze Iran- türkischen Grenze
Hoto: picture-alliance/AA/N. Hazar

Akalla mutum tara ne hukumomi suka tabbatar da mutuwarsu a girgizar kasar, inda masu aikin ceto ke kokarin taimaka wa mutanen da ibtila'in ya rutsa da su a yau Lahadi.

Akwai kuma wasu mutum 37 da suka jikkata,yayin da jiragen helikofta ke ci gaba da shawagi a yankuna masu sarkakiya.

Hukumomi sun ce babu wani da suke zaton ya makale a baraguzan gine-ginen da suka rushe, kamar yanda gwamnatin yankin na Van, Mehmet Emin Bilmez, ya shaidar.

Cibiyar nazarin bala'o'i masu nasaba da girgizar kasa ta nahiyar Turai, ta ce lamarin ibtila'in ya kai maki 5.7 a ma'aunin richter, kuma ya kai zurfin kilomita biyar.