Rashin tabbas a makomar gwamnatin Jamus
June 2, 2019Talla
Nahles ta fuskanci matsin lamba sakamakon koma bayan da jam'iyyar ta samu da ke zama sakamako mafi muni a zaben majalisar dokokin Tarayyar Turai a makon da ya gabata.
Ta ce za ta ajiye mukamin shugabancin jam'iyyar ta SPD a gobe Litinin, yayin da a ranar Talata kuma za ta sauka daga shugabancin rukunin 'yan jam'iyyar a majalisar dokoki.
Murabus din na bazata ya sanya ayar tambaya akan makomar gwamnatin kawance ta Angela Merkel wadda dama take tangal-tangal. A yanzu dai Jam'iyar SPD ta Andrea Nahles, da kuma CDU ta Angela Merkel sune ke gudanar da gwamnatin kawance a Tarayyar Jamus, kuma idan har SPD ta janye daga kawancen, hakan na nufin gwamnatin Angela Merkel ta wargaje.