1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wutar daji ta hallaka mutane a Girka

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 25, 2018

Rahotanni daga Girka na nuni da cewa mutane da dama ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wutar dajin da ta tashi a kauyen Mati da ke yankin Rafina a kasar ta Girka.

https://p.dw.com/p/324M3
Griechenland Waldbrände | Athen
Wutar daji ta haddasa asarar rayuka da ma dukiyoyi a GirkaHoto: Reuters/C. Baltas

Yankin na Rafina dai na da nisan kimanin kilomita 40 daga Athen babban birnin kasar ta Girka. Rahotanni da mahukuntan kasar suka bayar, na nuni da cewa kawo yanzu an gano kimanin mutane 190 da suka jikkata yayin da wutar dajin ta tashi sakamakon tsananin zafi da ake fuskanta a kasar. Jami'an kashe gobara na kasar da ke gudanar da aikin ceto, sun nunar da cewa suna ci gaba da binciken wadanda wutar dajin ta rutsa da su musamman a kauyen Mati da Kokkino Limanaki inda wutar tafi kamari. Kawo yanzu dai ana gab da shawo kan wutar, inda jami'an kwana-kwana na kasar ta Girka da wasu kasashe da ke makwabtaka da ita ciki har da Italiya, ke bada tallafi wajen ganin an kawo karshen wutar.