1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka na fuskantar barazanar sake zaɓe

Zainab MohammedMay 12, 2012

Har yanzu dukkanin jam'iyyun ƙasar sun gaza cimma matsaya kan kafa gwamnatin hadin kan ƙasa. Batu dake nuni da yiwuwar sake zaɓe a watan Yuni

https://p.dw.com/p/14uRb
epa03107488 Greek President Karolos Papoulias (C) is sitting among the military leadership during his visit to the Ministry of National Defence in Athens, Greece, 15 February 2012. In a strong reply to comments concerning the crisis in Greece which were made in recent days by a number of European officials, especially German Finance Minister Wolfgang Schaueble, the President of the Republic Karolos Papoulias stressed his displeasure at the tone adopted and the demands made to Greece. 'We all have an obligation to put our shoulder to the wheel in order to overcome the crisis. I cannot accept that my country should be reviled by Schaueble, I cannot accept this as a Greek', Papoulias said during a visit to the Greek defence ministry. He also urged the country's political class to prove itself worthy of its mission and to follow the example given by the military, underlining that saving Greece and its history was above all else. Earlier Finance Minister Evangelos Venizelos announced Papoulias' decision to stop receiving compensation for the performance of his duties. EPA/SIMELA PANTZARTZI pixel
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugaba Karolos Papoulias na Girka ya sake gayyato shugabannin jam'iyyun siyasar ƙasar, a wani yunƙuri na ƙarshe na hana sake gudanar da wani zabe. Hakan ya kasance ne, bayan da shugaban jam'iyyar gurguzu Evangelos Venizelos, ya zame shugaban jam'iyya ta uku daya sanar da gaza kafa gwamnatin haɗin gwiwa. 'Yan siyasan Girkan dai na fuskantar banbancin ra'ayi dangane da shirin tsuke bakin aljihu mako guda bayan kammala zaben kasar. Batu da a hannu guda ya bar wakilan majalisar dokokin suma da rarrabuwar kawuna, tsakanin masu goyon baya da kuma adawa da tsarin kuɗaden ceto na hadin gwiwar Kungiyar gamayyar Turai da hukumar bada lamuni ta IMF. Gazawar shugaba Karolos Papoulias wajen shawo kan jam'iyyun su kafa gwamnatin haɗaka, na nufin sake gudanar da zaɓe a watan Yuni. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a dai na nuni da cewar, mafi yawan al'ummar kasar na goyon bayan jam'iyyar dake adawa da tsarin ceton kasar daga matsalar karayar tattalin arziki, batu da ka iya illata wakilcin Girkan, a tsakanin gungun ƙasashe masu amfani da takardan kuɗi na Euro.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe