Girka na neman tallafin kuɗi Euro biliyan 45
April 23, 2010Girka ta bukaci ƙungiyar Tarayyar Turai da hukumar bada lamuni ta IMF da su sake tada batun shirin kuɗaɗen ceto ƙasar da ya kai Euro biliyan 45. Priminista George Papandreuo ya faɗawa gidan talabijin na Girka cewar, gwamnatinsa na hangen mawuyacin hanya gaba, dangane da haka ne ya zamanto wajibi su samu wannan kuɗin tallafin. Sai dai har yanzu ba a cimma matsaya dangane da ko nawa Girkan zata samu ba. Direktan IMF Dominique Strauss ya bayyana
cewar yanzu sun fara fara tattaunawa da hukumomin Girka, dangane da basu tallafi tare da haɗin gwiwar Turai, kuma nan da 'yan kwanaki masu gabatowa ne za a fara wannan tattaunawar.
A ranar 25 ga watan maris daya gabata nedai aka sanar da yarjejeniyar talafawa Girkar, tsakanin Tarayyar Turai da hukumar bada lamuni ta Majalisar Ɗunkin Duniya watau IMF.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Yahouza Sadissou