A Girka an bude kasuwannin hannayen jari
August 3, 2015Talla
Ƙasar Girka ta ɗauki mataki na gaba a batutuwa da sauka shafi tattalin arzikinta inda a ranar Litinin ɗin nan ta buɗe kasuwannin hannayen jarinta a karon farko, tun bayan da aka rufe kasuwannin makwanni biyar da suka gabata. Sai dai a yayin buɗe kasuwar ana tsammanin faduwar darajar hannayen jari.
Masu hada-hada a kasuwannin na hannayen jari a kasar ta Girka da ma wajenta na ganin cewa za a fiskanci faduwar darajar hannayen jarin da zarar an buɗe kasuwar a ranar Litinin din tun da misalin karfe bakwai agogon GMT.
A cewar Takis Zamanis masanin harkokin zuba jari a Girka ya ce ba sa tsammanin akwai wani hannun jari koda kuwa ɗaya ne da zai samu tagomashi a ranar Litinin ɗin nan da za a bude kasuwar.