Girka ta bukaci daukar karin matakan tsuke bakin aljihu
January 5, 2012Fraiministan Girka, Lucas Papademos ya yi kira ga kungiyoyin kodagon kasarsa da su amince da shirin rage albashi domin tabbatar da samun kashi na biyu na tallafin kungiyar Tarayar Turai da kuma asusun ba da lamuni na duniya. Yayin wata ganawa da ya yi da ma'aikata da wakilan ma'aikatu a birnin Athens, Papademos ya ce kasar ta Girka za ta shiga mawuyacin hali na tattalin arziki har bangarorin nan na uku dake tallafa mata suka ki su amince da ba da kashi na biyu na tallafin kudi. Su dai kungiyoyin kodagon sun yi watsi da wannan kira, suna masu cewa tuni ma'aikata da masu ritaya suka fara fuskantar matsala sakamakon rikicin tattalin arziki . A don haka babu wata dama ta rage albashi.
A tsakiyar watan Maris ne bangarorinin uku da suka hada da Kungiyar Tarayar Turai da asusun ba da lamuni na duniya da baban bankin Turai za su sake kai ziyara a kasar ta Girka. Bangarorin sun ce duk wani tallafin kudin da Girka za ta samu zai dogaroa ne akan shirinta na tsuke bakin aljihu.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu