1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka ta cafke masu safarar 'yan cirani

Zulaiha Abubakar
March 18, 2018

'Yan sandan kasar Girka sun sanar da tsare wasu mutane uku wadanda ke safarar 'yan cirani akan iyakar kasar da Iraki a yau Lahadi.

https://p.dw.com/p/2uYXZ
Flash-Galerie Illegale Migration nach Europa
Hoto: picture alliance / dpa

Sanarwar ta kara da cewar jami'an tsaron sun samu damar cafke mutanen uku ne bayan sun kutsa da 'yan ciranin da adadin su yakai 45 wadanda suka hada da maza da mata da kananan yara, da ga kasashen Siriya da Iraki zuwa cikin kasar ta Girka, ba bisa ka'ida ba ta hanyar amfani da wani jirgin ruwa.

A wani cigaban kuma rundunar 'yan sandan ta shaida wa manema labarai a yau cewar ta kuma samun damar kame wasu mutane biyu 'yan kasashen Afganistan da Pakistan a  filin jirgin saman Kavala da ke arewacin kasar ta Girka, dauke da fasfon kasar Jamus amma na jabu da kuma wani fasfo na Pakistan shi ma na bogi, yayin da suke kokarin tafiya zuwa kasar  Jamus.