1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka ta fasa jefa kuri'ar raba gardama

November 4, 2011

Bayan da shugabanin Turai suka sha mamakin sanarwar Frime Ministan Girka George Papandreou na gudanar da zaben raba gardama, a yanzu dai Girkar ta yi amai ta lashe domin ta fasa gudanar da zaben

https://p.dw.com/p/1359B
Frime Minista George PapandreouHoto: AP

A yayin da kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 ke shirin kammala taronsu a yau, Rahotannin da muke samu sun ce Girka ta soke shirinta na gudanar kuri'ar raba gardama dangane da kasancewarta mamba a rukunin kasashen da ke amfani da takardar kudin euro, matakin da yayi barazanar jefa rukunin kasashen cikin rikici. Ministan kudin Girkan Evangelos Venizelos wanda ya yi wannan bayanin, ya fadawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa kasar ta yi alkawarin dakatar da jefa kuri'ar ne lokacin wata ganawar da Jami'an ma'aikatar kudinta suka yi da shugaban rukunin kasashen da ke amfani da takardar kudin euron, Jean-Claude Juncker, da wasu manyan mahukuntan Tarayyar Turan ta wayar tarho. Hakanan kuma wata sanarwar da ta fito daga ofishin ma'aikatar kudin kasar ta sake bada tabbacin cewa kasar ba zata gudanar da kuri'ar raba gardamar ba. To sai dai majalisun Girka na nan na kada kuri'ar neman goyon bayan majalisar dokoki a kan Frime Ministan kasar George papandreou.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita          : Umaru Aliyu