1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka ta kama wani jirgin ruwa makare da makamai

Gazali Abdou TasawaSeptember 2, 2015

Rundunar sojin ruwan Girka ta kama wani jirgin ruwa makare da makamai marasa rijista da ke kan hanya zuwa kasar Libiya a jiya Talata.

https://p.dw.com/p/1GQA5
Waffen Libyen

Rundunar sojin ruwan kasar Girka ta bada sanarwar kama wani jirgin ruwa makare da makamai da ba su da rijista da ke kan hanya zuwa kasar Libiya a jiya Talata. Hukumomin kasar Girkan sun ce jirgin ruwan ya taso ne daga tashar ruwan Iskenderum ta kasar Turkiyya.

Kamfanin dillancin Labarai na Reuters wanda ya ruwaito labarin ya ce hukumomin kasar ta Girka sun tsare matukan jirgin su bakwai inda suka soma yi masu tambayoyi tare ma da kara binciken hajar jirgin ruwan da ake tsare da shi a tashar ruwan Heraklion ta kasa ta Girka.

Kasar Libiya dai wacce yanzu haka ke a karkashin ikon gwamnatoci biyu masu gaba da juna, na fuskantar takunkumin sayar mata da makamai wanda MDD ta kargama mata a wani mataki na neman kawo karshen fadan da kasar ke fama da shi tun bayan faduwar gwamnatin Gaddafi.