Girka ta sami karin wa'adi na watanni hudu
February 24, 2015Wadanda ke baiwa Girka bashi a kungiyar kasashe masu amfani da takardar kudin bai daya na euro, da ta kunshi kasashe 19 za sun amince da wasikar da ke kunshe da sauye-sauyen da Girka ta ce za ta gudanar domin a kara mata wa'adin samun kudaden ceton da watanni hudu, kuma ana sa ran zai taimaka wajen daidaita kasar da ma hana ta fita daga rukunin kasashen masu amfani da euro.
Da aka tambayi shugaban rukunin kasashen da ke amfani da takardar kudin Mr Jeroen Dijsselbloem ko yana ganin cewa Girka da gaske take yi ga abin da ya kada baki ya ce:
"A gani na da gaske suke, amma ba zai zo musu da sauki ba, wannan ne matakin farko, wannan wasika da suka aiko mana ba sabuwar yarjejeniya ba ce, abubuwan da suke fatan yi ne, ke nan wadanda suke so su maye wa gurbi da wadanda suke so su sauya. zai kuma dauki lokaci a ce an kulla wata sabuwar yarjejeniya"