1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka ta yi watsi da tayin Turai dangane da kasafin kudinta

January 29, 2012

Jamus ta shawarci kungiyar Tarayyar Turai da ta zabi kwamishana na musamman wanda zai rika sanya ido kan kasasfin kudin Girka

https://p.dw.com/p/13saM
Greek Minister of Finance Evangelos Venizelos delivers his speech during a parliament session, in Athens, on Wednesday, Sept. 21, 2011.Greece will have to take fresh austerity measures, the debt-ridden country's finance minister said Wednesday, a day after Athens moved a step closer to getting the vital bailout funds it needs to avoid a disastrous default next month. (Foto:Petros Giannakouris/AP/dapd)
Ministan kudin Girka Evangelos VenizelosHoto: dapd

Girka ta yi watsi da tayin da aka yi mata na mika ikon fada a ji kan alamuran da suka shafi kasafin kudinta ga hukumomin Turai. wani mai magana a madadin gwamnatin a Athens ya ce ko daya bai kamata ma a yi amfani da wannan tayi ba. Haka nan kuma wani kakakin hukumar ta Turai, shi ma ya nuna rashin amincewarsa. Duk wadannan ra'ayoyi sun biyo bayan wani tayi da Jamus ta gabatar wanda ya tanadi zaban wani kwamishana na musamman wanda zai sanya ido kan duk shawarwarin da Girka zata yanke kan kasafin kudinta. Mahukunta a Jamus sunce ana tattauna wannan batun a tsakanin ministocin kudin Turai a yanzu haka saboda gwamnati a Athens ta gaza cimma bukatun da suka wajaba a kanta, a karkashin yarjejeniyar farko wacce ta kamata ta taimaka mata wajen shawo kan matsalolin kudinta. A waje guda kuma cibiyoyin kudi masu zaman kansu na cigaba da tattaunawa da mahukuntan Girkan don ganin ko za'a yafe musu bashin euro milliyan dubu 100 a 'yan kwanaki masu zuwa.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Abdullahi Tanko Bala