1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka: Za a rufe sansanonin 'yan gudun hijira uku a kasar

Binta Aliyu Zurmi
November 20, 2019

Rahotanni da ke fitowa daga Girka na nuni da cewa, mahukuntan kasar za su rufe manyan sansanonin 'yan gudun hijira uku da ke wani tsibiri kusa da Turkiyya.

https://p.dw.com/p/3TQ5S
Griechenland Flüchtlingslager auf Lesbos
Hoto: Reuters/E. Marcou

A wata sanarwar da ya rabawa manema labarai, babban mai bayar da shawara ga harkokin 'yan gudun hijira a kasar Alkiviadis Stefanis, ya ce za ai hakan ne saboda yawan da 'yan gudun hijirar suka yi a sansanonin. Ya kara da cewa akwai sama da mutane dubu 27 da ke bukatar matsuguni mai kyau, ganin yadda sanyi ke karatowa.

Kasar ta Girka ta sha alwashin a farkon shekarar da ke tafe za ta canzawa akalla 'yan gudun hijira dubu 20 matsuguni wadanda ke cikin mawuyacin hali da kuma ake ganin  kasashen Turai sun yi watsi da su.

Bangaren gwamnati masu tsattsauran ra'ayi tuni suka yi sabuwar doka da za ta tsaurara al'amura ga 'yan gudun hijirar da ma shan alwashin mayar da su kasashensu na asali.