1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka za ta janye batun ƙuri'ar jin ra'ayi kan tsuke bakin aljihu

November 3, 2011

Firaministan Girka Georges Papandreou ya fara yunƙurin janye matakin kaɗa ƙuri'ar jin ra'ayi, a matakin magance matsalar basukan ƙasar

https://p.dw.com/p/134mZ
Firaministan Girka George PapandreouHoto: dapd

Firaministan Girka Georges Papandreou ya ce a shirye ya ke ya lashe amansa game dakirar da ya yi na gudanar da zaɓen raba gardama domin tantance makomar yarjejeniyar ceto tattalin arziƙin ƙasarsa da ya cimmma da ƙungiyar Gamayyar Turai. A lokacin wani taron majalisar ministoci da ya shugabanta a birnin Athenes a wannan alhamis, Papandreou ya yi alƙawarin watsi da duk wani mataki na kaɗa ƙuri'a, matiƙar 'yan adawa suka amsa kirar da ya yi musu na gudanar da shawarwari tsakinsu a majalisa domin ceto arzikin ƙasar da ke cikin mawuyacin hali.

Wasu daga cikin na hannun daman firimiyan ciki har da ministansa na kuɗi sun nesanta kansu daga matakin gudanar da ƙuri'ar raba gardama saboda karar tsaye da ya ke yi da manufofin Gamayyar Turai. Su kuwa jam'iyaun adawa sun nemi a gudanar da zaɓen gaba da wa'adi da nufin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa da za a ɗora wa alhakin ceto Girka daga mawuyacin hali da ta ke ciki. Firaminista Papandreou ya danganta wannan zaɓen da riga malam masallaci da zai ci gaba da tsunduma tattalin arzikin ƙasar cikin halin ni 'ya su.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Usman Shehu Usman