1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

COP26 : Soma taron kan matsalar dimamar yanayi

Abdoulaye Mamane Amadou
October 31, 2021

Kasashen duniya za su himmatu kan batun sauyin yanayi a babban taron koli na Majalisar Dinkin Duniya kan muhalli da za a soma gudanarwa a wannan Lahadi a birnin Glasgow.

https://p.dw.com/p/42OkR
Enlgland | COP26 | internationaler Klimagipfel in Glasgow
Hoto: Scott Heppell/AP Photo/picture alliance

A wannan Lahadi birnin Glasgow na Birtaniya ke karbar bakwancin kasashen duniya akalla 200 da ke soma taron kolin Cop26 na Majalisar Dinkin Duniya kan yanayi, da zummar ci gaba da tattauna yarjejeniyar kare muhalli ta birnin Paris. Manufar babban taron ita ce na rage hayaki mai haddasa dimamar yanayi da duniya ke fuskanta zuwa kasa da digo biyu.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa duniya na cikin wata mummunar barazana ta dimamar yanayi da ya zarta maki biyu da digo bakwai, lamarin da ya kai ta ga cewar dole sai an zage damntse. Ko baya ga Majalisar Dinkin Duniya kwararru kan yanayi da kungiyoyin rajin kare muhalli, sun yi ittifakin cewa matakan da duniya ke dauka a yanzu kan hayaki mai gurbata muhalli basu taka kara suka karya ba.