1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

GMF 2018: Fifiko a labaran ta'addanci

Umar Zahradeen Abdul-raheem Hassan
June 11, 2018

Mahalarta taron Global Media Forum da tashar Deutsche Welle ke shiryawa 'yan jaridun duniya duk shekara, sun koka kan yadda manyan kasashe ke nuna banbanci yayin ba da labaran ta'addanci.

https://p.dw.com/p/2zJRQ
Plenary Session How much inequality does a society need
Hoto: DW/U. Wagner

Wadanda suka gabatar da jawabai a babban taron sun nuna cewa akwai kimanin rikice-rikice da ke da alaqa da ta'addanci har 385 a sassan duniya daban-daban da ba a mayar da hankali akansu ba, shi ma Umar Sa'idu Tudun Wada shugaban gidan radiyon jihar Kano a Nijeriya ya nuna yadda kasashen Turai ke fifita kasashensu a wurin ba da rahotanni na ta'addanci fiye da sauran kasashe da ke fama da rigingimu da ya dara nasu.

Ute Schaeffer (DW Akademie, Interim Head, Germany) and Omar Mohammed (Mosul Eye, Founder, Iraq) | 09 | Session | Reporting terror: Who sees what, when and why?
Dan jarida a kasar Iraki, Omar MohammedHoto: DW/P. Böll

Omar Muhammad dan jarida ne da ya sha yin artabu da mayakan IS a kasar Iraki, ya kuma ce a fahimtarsa kafafen yada labaran duniya sun karkasa wadanda harin ISIS ke shafa zuwa gida-gida. "Rashin dai-daiton na fito wa fili a duk lokacin da ISIS ta kashe wani bature. A saboda haka ina fatan taruka akan yada labarai na duniya za su ci gaba da duba irin wannan maudu'i na nuna fifiko da kasashen Turai ke yi. Da zarar mun daina wannan dabi'a toh za mu gane su wane ne 'yan tadda."

Afra Naseer wata 'yar jaridar kasar Yemen, ta kasance daya daga cikin jami'ai hudun da su ka yi jawabi a wurin wanann taro, ta kuma nuna matsalar fahimtar asalin dan ta'adda. "Na yi imanin cewa muna da matsalar fahimtar wanene dan ta'adda, da kuma mutanen da aikace-aikacen ta'addancin ke shafa. Idan ka duba da kyau a kafafen yada labarai na kasa da kasa ana nuna bangaranci baro-baro."

Malam Umar Sa’id Tudun Wada (Kano State Radio Corporation, Managing Director, Nigeria) | 09 | Session | Reporting terror: Who sees what, when and why?
Shugaban gidan Rediyon jihar Kano, Mal. Umar Sa'id Tudun WadaHoto: DW/P. Böll

Irin wannan muhawara ce dai ta dauki hankalin taron da aka gudanar a cikin awa guda da wasu 'yan mintoci. Kuma 'yan jarida daban-daban sun ta yin tambayoyi akan yadda za a samu dai-daito a wurin magance matsalar. Sai dai  Umar Sa'id Tudun Wada, wanda ke ganin cewa "Mafita ita ce kafafen yada labarai su sake nazarin tsarin kundin aikinsu."

Wannan muhawara dai da aka tabka a wanann taro, da alama ta shiga zukatan 'yan jarida musamman na kasashen Turai, wadanda ake zargi da nuna fifiko kamar yadda Prita wata Bajamushiya mai horar da 'yan jarida ke cewa. "Abin da na koya dai a nan shi ne mutum ya kara zurfafa bincike akan bayar da rahoto na ta'addanci, domin har yanzu babu wata ma'ana kwaya daya da za ka ce ita ce ta'addanci. Lallai ya kamata mu duba dalilai na siyasa ko tattalin arziki da ke haddasa ta'addancin."

Taron Global Media Forum na shekarar 2018 shi ne taro karo na 11 da tashar DW ke shiryawa, tare da fatan 'yan jaridun duniya su fito da tsari mai adalci da zai fayyace abubuwan da ya kamata a kaucewa a yayin da ake ba da rahotanni da suka shafi ta'addanci.