Gobara ta ɓarke a wani kamapanin sarrafa ƙarafa na Kenya
September 25, 2007Talla
A ƙalla mutane 6 su ka rasa rayuka, a yayin da dama su ka ji raunuka, a sakamakon gobara da ta kunnu, a wani kampani sarrafa ƙarafa na ƙasar Kenya.
Gobara ta faru daga darenjiya zuwa sahiyar yau a kampanin Devic Steel Mills Limited, dake tazara kilomita 40 da Nairobi babban birnin ƙasar Kenya.
Gobara ta lalume wannan kampani baki ɗaya.
Hukumomin ƙasar Kenya, sun bayyana buɗa bincike, domin gano mussabbabin abukuwar ta.