Gobara ta hallaka mutane a Faransa
January 12, 2019Talla
Ministan cikin gidan Faransan Christophe Castaner ya ce biyu daga cikin wadanda suka rasu din ma'aikatan hukumar kashe gobara ne sannan 12 daga cikin mutum 36 da suka jikkata ke cikin matsanancin hali. Babban mai gabatar da kara na birnin na Paris ya ce bayanan da suka samu na nuna cewar gobarar ta tashi ne sakamakon fitar da iskar gas ta rika yi a gidan gasa burodin, lamarin da ya haddasa lalacewar gidan da kuma motoci da ke ajiye a gabansa. Tuni dai hukumomi suka ba da umarnin kwashe mutanen da ke zaune a gidajen da ke kusa inda wannan ibtila'i ya faru don gudun karuwar yawan mutanen da za su jikkata duba da irin yadda wajen ya turnike da hayaki.