1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gobara ta jikkata mutum 25 a Masar

October 2, 2023

Wata gagarumar gobara ta tashi a hedikwatar yan sanda a birnin Isma'iliya na kasar Masar inda akalla mutane 25 suka jikkata a cewar majiyoyin tsaro

https://p.dw.com/p/4X245
Masar | Gobara a ofishin 'yan sanda a Ismailia
Masar | Gobara a ofishin 'yan sanda a Ismailia Hoto: AFP/Getty Images

Rahotanni sun ce ba a sami hasarar rayuka ba kuma an sami shawo kan gobarar.

Bakin hayaki ya turnuke ginin a yayin da gobarar ta tashi.

Kawo yanzu dai ba a san musababbin tashin gobarar ba.

Ana dai yawan samun tashin gobara a Masar inda ake da karancin fadakarwa kan tashin gobara da kuma jinkiri wajen kai agajin gaggawa.

A watan Augustan 2022 gobara ta hallaka mutane 41 a wani coci a birnin Alkahira inda aka rika kiran samar da ingantattun kayan aiki ga ma'aikatan kwana kwana.