1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIndiya

Gobara ta kashe jarirai sabbin haihuwa a Indiya

May 26, 2024

Wata gobara da ta tashi a asibiti ta yi sanadin salwantar jarirai a kasar Indiya. Hukumomi da suka ce suna bincike kan lamarin, sun ce za su dauki matakin kotu a kan mai asibitin.

https://p.dw.com/p/4gI0i
Masu aikin ceto a wajen tashin gobara
Hoto: AFP/Getty Images

Rahotanni daga New Delhi babban birnin kasar Indiya, na cewa wata gobara ta tashi a sashen kula da jarirari na wani asibiti, inda ya zuwa yanzu jarirai sabbin haihuwa shida suka salwanta.

Jami'an tsaro musamman na 'yan sanda sun ce sun ceto wasu jarirai 12 su ma sabbin haihuwa, kuma ana ba su kulawa ta likita.

Jami'an sun kuma ce za a dauki mataki na shari'a a kan mamallakin asibitin, sai dai ba su ba da cikakken dalili ko karin bayani ba.

Cikin daren da ya gabata ne dai gobarar ta tashi, inda wuta ta yi muni saboda fashe-fashen tukwanen iskar Oxygen da ake tallafa wa marasa lafiya da su.

Ba a dai kai ga bayyana musabbabin tashin gobarar ba.