1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iTurkiyya

Gobara ta kashe mutane 66 a Turkiyya

Abdullahi Tanko Bala
January 21, 2025

Yawan mutanen da suka rasu a gobarar Turkiyya ya karu zuwa mutum 66. Wasu daga cikin mutanen sun rasu ne bayan da suka diro daga kan benen mai hawa goma sha biyu

https://p.dw.com/p/4pRfg
Iftila'in gobara a otel din wurin shakatawa da ke Kartalkaya a Turkiyya
Iftila'in gobara a otel din wurin shakatawa da ke Kartalkaya a TurkiyyaHoto: Mehmet Emin Gurbuz/Anadolu/picture alliance

Akalla mutane 66 suka rasu wasu mutum 50 kuma suka sami raunuka a wata gobara da ta tashi a wani otel a wurin shakatawa a arewa maso yammacin Turkiyya.

Gobarar ta tashi ne a wurin cin abinci na ginin mai hawa goma sha biyu da ke kan tsaunin Kartalkaya da misalin karfe uku da miniti 27 na dare.

Wasu daga cikin mutanen da lamarin ya ritsa da su sun rasu ne bayan da suka yi tsalle suka diro daga kan benen mai hawa goma sha biyu cikin firgici.