1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara ta kashe mutane a Paris

Abdul-raheem Hassan
February 5, 2019

Akalla mutane bakwai sun mutu sama da mutane 28 sun jikkata a hatsarin gobara da ta tashi a wani dogon bene mai hawa takwas da ke yankunan masu alfarma a yammacin birnin Paris.

https://p.dw.com/p/3CifY
Frankreich, Paris: Sieben Tote und ein schwer Verletzter nach Gebäudebrand
Hoto: Getty Images/G. van der Hasselt

Jami'an kashe gobara na birnin sun bayyana fargabar karuwar adadin asarar rayuka sakamakon mumnan rauni a yayin gujewa tirnikewar hayaki, ana dai cigaba da ayyukan ceto wadanda hatsarin ya ritsa da su. Sai dai kawo yanzu ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba, amma hukumomin sun kara tura jami'an gaggawa domin kwashe mutane da ke yankin.