Gobara ta salwantar da rayuka a Aljeriya
August 18, 2022Talla
Akalla mutane 26 ne rahotanni ke tabbatar da salwantar su sakamakon wutar daji da ta tashi a yankin arewa maso gabashin kasar Aljeriya.
Ministan harkokin cikin gida a Aljeriya, Kamel Beldjoud ya ce a lardin Al Tarf kadai, mutane 24 wutar ta kashe, yayin da a lardin Setif aka rasa mutum biyu.
Akwai ma wasu gomman da suka jikkata sakamakon kuna da kuma shakar hayaki mai tsanani da suka yi.
Hukumomi a Aljeriyar sun ce yankuna 39 ne ke fama da gobarar ta daji a cikin larduna 14, kuma 16 na a lardin Al Tarf ne.
Garin Sou Ahras, wanda ke iyaka da kasar Tunisiya ma na fama da gobarar da kawo yanzu jami'an kwana-kwana ta sauran jirage masu saukar angulu ke kokarin kawo karshenta.