1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara a babban sansanin 'yan gudun hijira da ke Girka

Binta Aliyu Zurmi MNA
September 9, 2020

Sama da mutum dubu 12 suka rasa matsuguninsu a sabili da gobarar a sansanin da ke Lesbos Sama da mutum dubu 12 suka rasa matsuguninsu a sabili da gobarar a sansanin da ke Lesbos.

https://p.dw.com/p/3iCQk
Griechenland, Lesbos: Brand im Flüchtlingslager Moria
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Balaskas

Gobara ta tashi a babban sansanin 'yan gudun hijira na tsibirin Lesbos da ke kasar Girka a wannan Laraba. Wutar ta fara ne kamar da wasa a lokacin da 'yan gudun hijirar ke bore game da dokar annobar Coronavirus da aka saka sanya musu.

Yanzu haka dai sama da mutum dubu 12 suka rasa matsuguninsu a sabili da gobarar. Wannan sansani ya yi kaurin suna wajen lalata wasu kayayyaki, hakan ya sa mahukunta fara bincike a kan abin da suka kira an saka wutar ne da gangan.

A yayin da ake kokarin samar musu da wani matsugunin an sami sama da mutane 35 da suka kamu da cutar Covid-19 a sansanin.