1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKenya

Gomman masu zanga-zanga sun mutu a Kenya

June 29, 2024

Zanga-zangar adawa da matakin karin haraji a Kenya ya yi sanadin salwantar rayukan mutane da dama, a cewar kubgiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch.

https://p.dw.com/p/4heub
Masu bore a birnin Nairobi na ksar Kenya
Masu bore a birnin Nairobi na ksar KenyaHoto: Daniel Irungu/EPA

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch, ta ce akalla mutane 30 ne suka salwanta a zanga-zangar da matasan kasar Kenya suka kira cikin wannan mako, bayan shirin gwamnati na kara haraji.

Kungiyar ta ce jami'an tsaron kasar ta Kenya dai sun yi ta harbi kai tsaye zuwa cikin dandazon jama'ar da ke zanga-zangar a ranar Talatar da ta gabata, ciki har da wadanda ke kokarin tsaerewa daga cikin su.

Sanarwar da Human Rights Watch din ta fitar ta kuma nuna cewa bude wuta kai tsaye da jami'an suka yi, ya saba ka'ida; sannan bugu da kari ba su ma kyale hatta masu boren da ke kokarin guje wa yamustin ba.

A jiya Juma'a ma dai wasu 'yan gwagwarmaya a Kenyar, sun yi kiran da a fito domin sabuwar zanga-zangar tare da yajin aiki, har sai Shugaba William Ruto ya sauka daga mukaminsa, duk kuwa da janye matakin karin harajin da ya dauka.