1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: Nakiya ta salwantar da rayuka

September 6, 2022

A Burkina Faso, kimanin fararen hula 35 ne suka mutu ya yin da wasu 37 suka jikkata sakamakon taka nakiya da motarsu ta yi a arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4GSTU
Benin | Fotoreportage Marco Simoncelli aus Porga
Hoto: Marco Simoncelli/DW

A cikin sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar, ta ce, hatsarin ya faru ne a tsakanin garuruwan Djibo da kuma Bourzanga.

Mutanen dai sun gamu da ajalinsu ne yayin da suke kan hanyar zuwa babban birnin kasar Ouagadougou, kana yawancinsu 'yan kasuwa ne da kuma dalibai da za su koma makaranta daga hutu. 

Ko a farkon watan Agustan da ya gabata, dakarun soji 15 ne suka mutu a wani harin da 'yan ta'adda suka kai a kan hanyar Dori zuwa Djibo da ke arewacin kasar.

Kasar Burkina Faso dai ta shafe tsawon shekaru 7 ta na fama da matsaloloin masu tada kayar baya wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 2000 yayin da wasu kimanin miliyan 2 suka rasa matsugunnansu.