1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gomman mutane sun mutu a Chadi

October 20, 2022

Sabbin alkaluma da ke fitowa daga Chadi na cewa kimanin mutum 50 suka mutu, wasu gommai kuwa suka jikkata sakamakon zanga-zangar adawa da sabuwar gwamnatin riko a kasar.

https://p.dw.com/p/4IUWB
Tschad | Proteste in Ndjamena
Hoto: Blaise Darioustone/DW

Daruruwan mutane ne suka yi dafifi a N'Djamena babban birnin Chadin, suna bukatar sojojin kasar da su mutunta alkawarin mika mulki ga gwamnatin farar hula, maimakon kara wa kansu wa'adin shekaru biyu da suka yi.

Majiyoyin lafiya sun tabbatar da mutuwar mutanen sanadiyar harbin bindiga da ma hayaki borkonon tsohuwa da jami'an tsaro suka yi amfani da su a kan masu boren.

Tun da farko dai masu zanga-zangar sun lalata motoci da sauran nau'uka na ababan hawa tare ma da farfasa shagunan ‘yan kasuwa abin da ya kara munana lamarin a Chadi.

A ‘yan kwanakin da suka gabata ne aka gudanar da taron kasa domin sama wa Chadi makoma, taron da ya bayanna Shugaba Mahamat Idriss Deby a matsayin shugaban kasa na riko, shugaban kuma ya nada madugun adawa Saleh Kebzabo a matsayin firaminista.