Goodluck Jonathan ya yi tir da harin Kano
April 30, 2012Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa kiristoci a Jami'ar Bayero ta Kano, wanda ya salwantar da rayukan mutane aƙalla 20. Cikin wata sanarwa da fadar mulkin ta Abuja ta fitar da wannan litinin, Jontahan ya yi kira ga talawakawan ƙasarsa da su ci gaba da yin tir ga ayyukan tarzoma da ke ci gaba da zama ruwan dare a yankin Arewacin Najeriya.
Shugaban ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukan duk matakan da suka wajaba domin ganin bayan ayyukan ta'addaci a ƙasar da ta fi yawan al'uma a nahiyar Afirka. Duk da cewa babu wata ƙungiya da ta yi iƙirarin kai hari na kano, amma kuma ana alaƙantashi da ƙungiyar Jama'atu Ahlisnnah Lidda'awati Waljihad da aka fi sani da suna Boko Haram.
Sai dai kuma wannan sanarwa ta Jontahan ta zo ne a daidai lokacin da mutane da dama suka rasa rayukansu a Jalingo, babban birnin jihar taraba, sakamakon tayar da bama-bamai da wasu 'yan bindiga suka yi da safiyar wannan litinin a hedkwatar 'yan sandan jihar ta tarabar.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala