1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'aziyyar mutuwar Mikhail Gorbachev

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 31, 2022

Shugabannin kasashen duniya, na ci gaba da mika sakon ta'aziyyarsu da kuma nuna alhini kan mutuwar tsohon shugaban Tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev.

https://p.dw.com/p/4GH1M
Mikhail Gorbachev ya rasu
Fitaccen gwarzo Mikhail GorbachevHoto: Sergei Karpukhin/REUTERS

Mikhail Gorbachev da ke zaman shugaban Tarayyar Soviet na karshe dai, ya rasu yana da shekaru 91 a duniya. Gorbachev dai na shan yabo kan yadda ya kawo karshen yakin cacar baka, inda aka bayyana shi da shugaban da ba ko yaushe ake samun irinsa ba. Da yake mika sakon ta'aziyarsa Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana shi a matsayin dan siyasar da duniya ba za ta manta da gudunmawarsa ba, yana mai cewa ya jagoranci kasarsu a lokacin da take cikin halin tsaka mai wuya. Putin ya kara da cewa Gorbachev ya fahimci rudanin da ake ciki, kuma ya yi kokarin kawo mafita ga abubuwan da suke bukatar gyara cikin gaggawa. Shi ma shugaban Amirka Joe Biden ya yabawa tsohon shugaban na Tarayyar Soviet, wanda ya bayyana a matsayin gwarzo.

A nasa bangaren shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana cewa, Jamus na matukar alfahari da Gorbachev kan rawar da ya taka wajen sake hadewar kasar. A jawabinsa shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yabawa Gorbachev kan rawar da ya taka a Jamus yana mai cewa: "Ya kasance shugaba mai karfin hali da jajircewa wajen kawo sauyi, ya kawo ci-gaba ba ma wajen bunkasar dimukuradiyya a Rasha ba har ma da Turai baki daya. Ya mutu a lokacin da Shugaba Vladmir Putin ya kawo rikici a Rasha da ma Turai duka, ta hanyar kai hari a makwabciyar kasarsa Ukraine."

Ita ma a nata bangaren tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel da ta taso a yankin gabashin Jamus, ta bayyana cewa Gorbachev ya kawo gagarumin sauyi a rayuwarta ya kuma nuna yadda bayani guda ka iya kawo gagarumin sauyi da ci-gaba a duniya.