1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zimbabuwe: Ambaliya ta kashe mutane 31

Abdul-raheem Hassan MAB
March 17, 2019

Majalisar Dinkin Duniya na yunkurin ceto dubban mutane da ambaliyar ruwa da guguwa suka shafa a Kudu maso arewacin Afirka, inda mutane da dama suka mutu a yankin kawo yanzu.

https://p.dw.com/p/3FCKK
Malawi Zyklon Idai
Hoto: Getty Images/AFP/A. Gumulira

Akalla mutane 31 sun mutu a gabashin Zimbabuwe sakamakon wata mahaukaciyar guguwa da ruwan sama mai tsanani, wadanda suka karya gadoji da lalata gidaje bila adadin.

Kusan mutane 40 sun bata bayan da guguwar ta shafe makonni tana barazana ga wasu kasashen a Kudu maso gabashin Afirka, ta kuma barnata turakan lantarki da layukan sadarwa a tsakanin kasashen Zimbabuwe da Mozambik.

Gwamnati ta ba da umarnin kwashe mutane da ke zaune a yankunan da ibtila'in ya faru da wadanda ke kusa da tsaunuka ba. Amma karfin iska na hana masu ayyukan agaji kai dauki da jiragen sama.