Mutane shidda sun rasa rayukansu a Girka
July 11, 2019Talla
Gabanin faruwar wannan ibtila'i dai wata iska mai karfi ce ta fara kadawa a arewa maso gabashin yankin Halkidiki wacce ta haifar da rushewar manyan gine-gine da fizgo bishiyoyi tun daga tushe da kuma kifar da ababen hawa, a nata bangaren hukumar kula da yanayi a kasar ta Girka ta bayyana cewar wannan shine karon farko da kasar ta fuskanci irin wannan iska mai karfin gaske a tarihi duk kuwa da yanayin zafi da ake ciki. Daga cikin wadanda suka rasa rayyukansu har da 'yan yawon bude ido daga kasashen Rasha da Romaniya.