1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwa ta hana tashin jiragen sama a Jamus

Abdul-raheem Hassan
February 9, 2020

Wata guguwa mai karfin gaske da aka yiwa lakabi da Sabine, ta doso kasar Jamus da wasu kasashen nahiyar Turai bayan da ta wuce Birtaniya da Ireland.

https://p.dw.com/p/3XUZm
Frankfurt am Main | Lufthansa Airbus A321-231
Hoto: Imago Images/R. Wölk

Yanzu haka guguwar ta tilasta dakatar da sauka da tashin jirage kusan 100 a babban filin jirgin sama na Frankfurt.

Kamfanin sufurin jiragen sama na Lufthansa ya sanar da yiwuwar soke tashi da saukar jirage daga ranar Lahadi har zuwa ranar Talata saboda fargabar barnar da guguwar za ta haifar.

Hukumomi sun yi garagdin guguwar Sabine da ta taso daga tekun Atlantika na gudun kilomita 120 a sa'a guda, kuma za ta iya haddasa ruwan sama da tsawa a wasu sassan nahiyar Turai.