1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Guguwa ta sa Joe Biden dage ziyararsa zuwa Jamus da Angola

Mouhamadou Awal Balarabe
October 8, 2024

Sanarwar fadar mulki ta White House ta ce "Milton" na iya zama guguwa mafi muni da Florida za ta fuskanta a karni guda, saboda hake ta yi kira ga mazauna yankin da suka kaurace wa gidajensu don gudun salwantar rayuka.

https://p.dw.com/p/4lYT2
Guguwar "Milton" da ta durfafi Florida ta sha Joe Biden da mukarabbansa kai a White House
Guguwar "Milton" da ta durfafi Florida ta sha Joe Biden da mukarabbansa kai a White HouseHoto: Evan Vucci/AP Photo/picture alliance

Shugaba Joe Biden na Amurka ya dage balaguron da ya tsara gudanarwa a karshen mako a Jamus da Angola domin daukar matakan tinkarar mahaukaciyar guguwar "Milton" da ta durfafi kasarsa. Sanarwar da fadar mulki ta White House ta bayar ta ce "Milton"  na iya zama guguwa mafi muni a Florida za ta fuskanta a cikin karni guda, saboda hake ta yi kira ga mazauna yankin da suka kaurace wa matsugunansu don gudun salwantar rayuka.

Karin bayani:Mahaukaciyar guguwa ta yi barna a Amurka 

Masana yanayi na sa ran guguwar "Milton" ta isa Florida a ranar Laraba, lamarin da ke haifar da barazana ga rayuka. A yanzu haka tana kadawa a mashigin tekun Mexico da ke gabar teku, kuma karfinta ya kai kusan kilomita 250 a cikin sa'a guda. Sai dai iftila'in na iya zamawa karfen kafa a siyasance, a daidai lokacin da ya rage wata guda da gudanar da zaben shugaban kasar Amurka, saboda guguwar "Helene" ta kashe mutane 210 a kudu maso gabashin kasar.