1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iska da ambaliyar ruwa a Pilipin

Abdul-raheem Hassan
September 16, 2018

Akalla mutane 36 sun mutu yayin da ake fargabar zabtarewar kasa ya rufta da masu hako ma'adinai da dadama sakamakon bala'in guguwar Typhoon Mangkhut da ta afkawa kasar Pilipin.

https://p.dw.com/p/34xIQ
Philippinen Taifun Mangkhut
Hoto: Imago/ZUMA Press/P. Torres

Hukumomin 'yan sanda a gabashin kasar sun ce guguwar ta haddasa tsananin iska da ambaliyar ruwa mai karfi, abinda ke hana ayyukan ceto rayukan mutane da da gidaje da itatuwa suka fada kansu.

Guguwar Mangkhut ta fara iso wasu yankunan nahiyar Asiya a kan gudun kilomita 162 a sa'a guda, inda tuni kasar China ta fara kwashe daruruwan 'yan kudancin kasar tare da dakatar da zirga-zirgar jirage.