Guido Westerwelle yana fatan samun zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya
May 24, 2010Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yayi kira ga shugabannin yankin gabas ta tsakiya dasu bada tasu gudumawar wajen kawo zaman lafiya a yankin.
A ƙarshen ziyarar daya kai yankin, Westerwelle ya gana da Sarki Abdallah na biyu na Jordan da shugaban Syriya Bashar al-Assad da nufin ganin sun taimaka wajen shirya ganawa ta ƙeƙe da ƙeƙe tsakanin Israilawa da kuma Palasɗinawa.
A lokacin ganawar tasu ministan harkokin wajen na Jamus yayi kira musanman ga Syriya data nisanta kanta daga ƙungiyoyi masu tsattsuran ra'ayi da basa ƙaunaran ganin anyi wannan ganawar.
Tunda farko dai saida Westerwelle ya gana da shugaban Masar Husni Mubarak a ranar Asabar bayan ya ziyaraci Lebanon. A yau litinin itama shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel zata fara ziyara a yankin gabas ta tsakiya.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Yahouza Sadissou Madobi