1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dadis Camara zai iya fuskantar hukuncin daurin rai-rai

Abdourahamane Hassane
May 22, 2024

Mai gabatar da kara a shari'ar tarihi na kisan gillar da aka yi a kasar Guinea a ranar 28 ga watan Satumban na shekara ta 2009 ya bukaci da a yanke hukuncin daurin rai-rai wa Dadis Camara.

https://p.dw.com/p/4gA7k
Moussa Dadis Camara
Moussa Dadis CamaraHoto: epa/dpa/picture alliance

 Mai gabatarda karan ya bukaci da a yanke hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari kan wasu mutane uku da ake tuhuma, da kuma shekaru 14 a kan wasu mutane biyu.Akalla mutane 156 ne aka kashe ta hanyar harbin bindiga, ko wuka, ko adduna  sannan daruruwa suka jikkata sakamakon murkushe masu zanga-zangar adawa a wani filin wasa kwallon kafa na Conakry  a ranar 28 ga Satumba, na shekara 2009 wanda ake zargin Dadis Kamara da laifin ba da umurnin kisan.