1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum bakwai sun mutu a Guinea a saboda zanga-zanga

May 14, 2020

Akalla mutum bakwai wadanda suka hada da 'yan sanda da fararen hula suka salwanta biyo bayan wata zanga-zanga da jama'an gari suka yi a yankunan Coyah da Dubreka da kuma Kamsar na kasar Guinea Conakry.

https://p.dw.com/p/3cByH
Guinea Conakry Demonstration Ausschreitungen Polizei
Hoto: AFP/C. Binani

Jama'a dai sun fito kan tituna suna korafi a kan rashin wutar lantarki a gidajensu a cikin dokar kulle da mahukumta suka sanya. Kazalika masu zanga-zangar sun bukaci gwamnati da ta janye shingayen jami'an tsaro da aka sanya don hana jama'a zirga-zirga a wannan lokaci. To amma daga bisani sai zanga-zangar ta rikide ta koma tashin hankali. 

'' A lokacin da mu mata muka zo kasuwa sai muka ji  jami'an tsaro sun fara harbe harbe, suna kuma watso mana barkonan tsohuwa. Hudu daga cikin 'ya'yanmu da aka harbe sun mutu kuma asibiti ya ki karbar gawarwakinsu. Amma mu zamu kalubalanci wannan lamari har sai sun karbi gawawwakin.'' inji Adama Socko, daya daga cikin masu zanga-zangar.

Tuni dai gwamnatin Guinea Conakry ta yi Allah-wadai da wannan harbe-harbe da kuma zanga-zangar. Kawo yammacin Larabar nan kasar na da mutum 2,374 masu coronavirus, mutum 14 kuma suka mutu daga cikin wannan adadi.