1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

060511 9-11 Spurensuche GB

August 8, 2011

Bayan harin ta'addancin da aka kai birnin London a shekara ta 2005 da waɗanda aka yi niyyar kaiwa a wasu ƙasashen Turai, ya da ƙasashen yammaci sun fargaba a game da 'yan ta'adda na cikin gida.

https://p.dw.com/p/12D3I

A Birtaniya akwai gungun musulmi masu zazzafar aƙida a Luton, wani ɗan ƙaramin gari dake arewa da birnin London. To sai dai kuma su kansu mazauna garin ra'ayinsu ya banbanta inda suke zargin yunƙurin shafa wa garin nasu kashin kaza game da kasancewa wani sansani na 'yan ta'adda.

A ƙofar wani gida ke nan a wani yanki mai natsuwar gaske dake garin Luton mai tazarar tafiyar awa ɗaya daga birnin London. A misalin shekara ɗaya da ta wuce wani magidancin da ake kira Taimour Abdulwahab al-Abdaly ya bar gidan inda ya kama hanyarsa zuwa ƙasar Sweden.

A can cibiyar garin Stockholm dake ɗoki da murnar ƙaratowar bikin kirsmeti ya tarwatsa motarsa sannan ya kuma tarwatsa kansa da kansa. Alhakin da aka ɗora masa, kamar yadda ya nunar, shi ne ya kashe farar hula na ƙasar Sweden, a matsayin ramuwa akan tura sojojinta zuwa Afganistan da ƙasar Sweden ta yi. Ya dai bar bayani a baya, inda yake cewar:

Ausbreitung des islamistischen Terrors in Luton England
Abdul Qadeer Baksh limamin masallacin LutonHoto: DW/L.Bevanger

"Goyan bayan da kuke ba wa sojojinku shi ne ya janyo muku wannan bala'in. Ina kuma roƙon Allah Ya amince da shahada ta."

A dai kusa da gidan su Al-Abdaly a Luton akwai masallacin da ya saba salla a cikinsa. Abdul Qadeer Baksh shi ne limamin masallacin:

"Ya yaɗa fassarar da ba ta dace da musulunci ba ya kuma yaɗa zazzafar aƙida a sakamakon haka na gana da shi na kuma nuna masa ra'ayina. Na yi haka ba sau ɗaya ba sau biyu ba, sannan wata rana bayan sallar asuba na tsayar da shawarar tattaunawa da shi a bainar jama'a. A ƙarshe dai hankalinsa ya tashi ya kuma bar masallacin a cikin fushi. Tun daga sannan ban sake ganinsa ba."

Ta'addanci na gama gari ko ɗaiɗaikun mutane

Shi dai mai alhakin harin na Stockholm ɗaya ne daga cikin masu zazzafar aƙidar addini da yawan gaske, waɗanda suka ɓata wa Luton suna. A shekara ta 2009 wani gungu na musulmi sun yi cincirindo suna la'antar sojojin Birtaniya dake dawowa daga Iraƙi. Sun musulta su tamkar sarakan yanka, 'yan kisan-kiyashi da kisan kai. Hakan ta haifar da wata ƙungiya mai ƙyamar musulmi, wadda ake kira wai ƙungiyar kare kan Ingila EDL ta kuma yi ƙaurin suna yanzu haka.

"Wannan ƙasarmu ce! England, England, England!"

Ausbreitung des islamistischen Terrors in Luton England
Gaban gidan da Taimour Abdulwahab al-Abdaly ya ajiye motarsa ya tafi Sweden ya ƙaddamar da harin ta'addanciHoto: DW/L.Bevanger

"Duka-duka bai wuce mutane goma sha biyar ko sha takwas da suka ci mutuncin sojojinta ba. Kuma wannan shi ne ainhin adadin waɗanda ake kwatantawa da kasancewa masu zazzafar aƙida a Luton. Kazalika ita ma EDL yawan magoya bayanta a Luton bai taka kara ya karya ba. Amma kafofin yaɗa labarai na yayata maganar fiye da ƙima."

Luton ba dandalin masu zazzafar ra'ayi ba ne

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Zafar Kahn shugaban majalisar addinai dake adawa da rarrabuwar kawunan jama'a a Luton. Bisa ga ra'ayinsa ba a kamanta gaskiya ba wajen kwatanta Luton tamkar wani dandalin ƙyanƙyashe masu zazzafar aƙidar addini. Ita ma dai ƙaramar hukumar Luton ta damu matuƙa ainun a game da shafa wa sunan garin kashin kaza da ake yi. A sakamakon haka hukumar ta tashi tsaye wajen shirya bukukuwan al'adu domin bayyana wa mutane irin kyakkyawan zaman cuɗe-ni-in-cuɗe-ka da ake yi tsakanin jinsuna daban-daban da garin ya ƙunsa. Sai dai kuma duk da haka ita Birtaniya kanta za ta ci gaba da fuskantar barazana daga 'yan ta'adda, lamarin dake ma'anar cewa jami'an tsaro a dukkan biranen ƙasar dake da ɗimbin musulmi, za su ci gaba da sa ido akan kai-da-komon jama'a. Mai yiwuwa mazauna garin Luton su haƙura da hakan, amma kuma tilas ne su ci gaba da fafutukar wanke sunan garin nasu.

Mawallafa: Lars Bevanger / Ahmad Tijani Lawal
Edita: Mohammad Nasiru Awal