1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres: UNRWA na nan daram, babu sauyi

Abdullahi Tanko Bala
October 29, 2024

Antonio Guterres ya ce haramta aikin UNRWA ka iya yin mummunar illa ga yan gudun hijira Falasdinawa, inda ya ce ba za su lamunci Isra'ila ta haramta aikin UNRWA a yankin Falasdinawa ba .

https://p.dw.com/p/4mMVy
Hukumar UNRWA a birnin Kudus
Hoto: Ilia Yefimovich/picture alliance/dpa

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce dokar Isra'ila ta haramta aikin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA zai iya haifar da mummunan sakamako ga Falasdinawa 'yan gudun hijira a yankunan da Isra'ila ta mamaye. Yana mai cewa ko kadan ba a lamunci hakan ba.

Guterres ya ce yayin da ake cikin wannan tsanani, aikin UNRWA ya fi zama wajibi a yanzu fiye da kowane lokaci a baya kuma ba za a iya maye gurbinta ba. Ya ce aiwatar da wadannan dokoki da Isra'ila ta yi zai kasance koma baya ga yunkurin warware rikicin Isra'ila da Falasdinawa don dorewar zaman lafiya da tsaro a yankin baki daya. Guterres ya ce zai gabatar da batun ga babban zauren Majalisar Dinkin Duniya mai wakilan kasashe 193