1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ba ta ji dadin yadda rikicin Ukraine ya kai watanni 6 ba

August 24, 2022

A jawabin da ya yi wa kwamitin sulhu na majalisar albarkaci cika watanni shida da fara yakin, Guterres, ya ce radadin rikicin bai tsaya ga Ukraine kadai ba, inda ya ce tuni tasirin mamayar ya sauya al'amura a duniya.

https://p.dw.com/p/4Fzs3
Ukraine | Antonio Guterres und Wolodymyr Selenskyj | Treffen in Lemberg
Hoto: Ukrainian Presidency/AA/picture alliance

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya siffanta watanni shida da Rasha ta kwashe tana yaki da Ukraine a matsayin wani babban abin takaici.

'' A cikin wannan lokaci mai tsanani, dubban fararen hula aka kashe, an kuma raunata wasu ciki har da kananan yara. Iyalan da suka rasa masoyansu ba za su irgu ba. Duniya ta shaida keta hakkin dan Adam na 'inna-naha'' ba tare da wani dalili ba.'' in ji Guterres

Sai dai lokacin da Sakatare Janar na MDD ke nuna takaicinsa kan rikicin ne, rahotanni suka ce Rasha ta kai sabon hari mai muni a kan wani layin dogo da ke tsakiyar Ukraine. Sai dai shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya lashi takobin cewa kasarsa za ta ci gaba da kare kanta har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi.