1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres ya yi gargadi kan makamin nukiliya

Abdullahi Tanko Bala
February 6, 2023

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce yana fargaba duniya na tunkarar gagarumin rikici da ba a san iyakarsa ba

https://p.dw.com/p/4NAKY
Ägypten | UN Weltklimakonferenz COP27 | Antonio Guterres
Hoto: Christophe Gateau/dpa/picture alliance

Antonio Guterres ya baiyana fargabar yaduwar yakin Ukraine a yayin da yake jawabi gaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York yayin da ake dab da cika shekara guda da barkewar yakin. 

"Ya ce mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine na haifar da wahalhalu mara misali ga mutanen Ukraine da kuma karin tasiri a duniya baki daya. Hasken samun zaman lafiya na gushewa, kamarin fadan da zubar da jini na karuwa. Ina fargabar duniya na kara dulmiya cikin yakin da ke kara yin fadi".

Da ya juya ga barazanar Rasha na yin amfani da makaman nukiliya, Antonio Guterres ya ce duniya na bukatar zaman lafiya. Amfani da makamin nukiliya wauta ne, muna cikin hadari na gomman shekaru na yiwuwar barkewar amfani da makamin nukiliya walau da sani ko kuma bisa kurkure.