Ganawa tsakanin Guterres da Putin
April 26, 2022A wannan Talata aka tsara Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres zai gana da Shugaba Vladimir Putin na Rasha a birnin Moscow fadar gwamnatin kasar domin tattauna hanyoyin diflomasiyya na kawo karshen yakin da aka kwashe watanni biyu ana fafatawa bayan Rasha ta kaddamar da kutse a kan Ukraine.
Tattaunawar ta fadar Kremlin za ta mayar da hankali kan rawar diflomasiyya da Majalisar Dinkin Duniya bisa warware yakin da ke faruwa a Ukraine, gami da samar da hanyoyin da za a samar da mafita ga fararen hula da suke wuraren yaki ya yi zafi.
Kana babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai shekaru 74 da haihuwa zai gana da Sergei Lavrov ministan harkokin wajen kasar ta Rasha. Tun farko dai Babban jami'in MDD ya gana da Shugaba Recep Erdogan na Turkiyya a kan hanyar tafiya kasashen da ke samun sabani da juna.
Daga Rasha, sai kuma António Guterres babban jami'in na MDD ya zarce zuwa kasashen Poland da Ukraine, inda ake sa ran zai gana da Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar ta Ukraine ranar Alhamis mai zuwa.