Gwagwarmaya kan Aleppo
July 4, 2015Dakarun gwamnatin Siriya sun kara da 'yan tawayen da ke ciki da wajen Aleppo, a kokarin da gwamnatin ke yi na ganin ta rage karfin kungiyar IS musamman a wuraren da take da karfi kamar Aleppo.
Gwamnatin ta kaddamar da sabbin hare-haren ne ranar Juma'a a matsayin wani martani ga sabuwar hadakar kungiyoyi 13 da aka kulla, wadanda suka hada har da wani reshe na kungiyar Al-ka'ida, mai suna Nusra Front, da sauran kungiyoyin tawaye. Wannan hadakar kungiyoyin da suka sanya wa suna Ansar al-Sharia ta ce burin ta shi ne 'yantar da Aleppo, wanda ya kasance cibiyar cinikayya da masana'antu.
Tashe-tashen hankulan kasar dai sun kai ga raba wannan birbi zuwa gida biyu, yankin gabashin da ke karkashin 'yan tawaye da kuma yammacin wanda ke karkashin ikon gwamnati